Video game: Sony ya sayi OnLive

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Sony ya sayi kamfanin OnLive, mai yin na'urar wasa ta Video game

Kamfanin OnLive wanda yake sahun farko wajen harkar na'urar wasan video game a duniya ya sayar wa da Sony hajar tasa.

A baya dai kamfanin ya kai darajar kudi har dala biliyan daya da digo takwas, kwatankwacin fan biliyan daya da digo biyu.

Kawo yanzu dai ba a bayyana yadda cinikin ya kaya ba.

A shekarar 2012 dai ma'aikatan kamfanin na OnLive masu yawa suka rasa ayyukansu sakamakon bashin da ake bin kamfanin har na kudi kusan dala miliyan 40.