An sace dan Romania a Burkina Faso

Shugaban riko na Burkina Faso Michel Kafando Hakkin mallakar hoto
Image caption Ba a cika ganin irin wannan lamari ba a Burkina Faso

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun yi awon gaba da wani wani jami'in tsaro dan Romania dake aiki a wata mahakar ma'adinai a Burkina Faso.

An dai sace shi ne yayin da suke bakin aiki kusa da garin Tambao, a wani hari da ya yi sanadiyyar jikkatar direban motar da jami'in tsaron yake ciki, da kuma dan sanda daya.

Ma'aikatar harkokin wajen Romania ta tabbatar da sace dan kasar tata, kuma ta ce ana duba batun.

Masu aiko da rahotanni sun ce yayin da ake sace baki 'yan kasashen waje akai-akai domin karbar kudaden fansa a kasashen Mali da Nijar masu makwabtaka da kasar, hakan bai cika faruwa a Burkina Faso ba.