PDP ta kori mataimakin gwamnan Jigawa

Image caption Jam'iyyar ta zargi Alhaji Ahmad Mahmud da yi mata zagon kasa a zabe

Jam'iyyar PDP ta kori mataimakin gwamnan jihar Jigawa da ke Najeriya,Alhaji Ahmad Mahmud a kan zargin yi mata zagon kasa a zaben majalisar dattawa da ka yi.

Jam'iyyar ta zargi Alhaji Ahmad Mahmud da kin zabenta a zaben 'yan majalisar dattawan kasar da aka yi ranar 28 ga watan Maris.

Masu ruwa da tsaki na mazabar gwamnan ta Galagamma da ke Gumel ne suka dauki matakin, wanda kuma reshenta na karamar hukumar ya amince da hukuncin.

Kokarin da BBC ta yi na jin ta bakin mataimakin gwamnan ya ci tura domin wayarsa tana rufe.