Boko Haram ta kai hari a kan kauyukan Borno

Rahotanni na cewa an kai harin ne da daren ranar Lahadi.
Bayanan hoto,

Rahotanni na cewa an kai harin ne da daren ranar Lahadi.

Mazauna garin Kwajaffa da ke karamar hukumar Hawul ta jihar Bornon Najeriya sun ce wasu da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kai musu hari, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Kazalika, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kai hari a kan wasu kauyuka da ke karamar hukumar Kala Balge.

Mutanen da BBC ta yi hira da su a Kwajaffa sun ce an kai harin ne a daren ranar Lahadi, kuma an kona wasu sassan garin.

A cewarsu, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun tara mutane wuri guda suka yi musu wa'azi, sannan daga bisani suka kashe su.

Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka mutu a wuraren da aka kai hare-haren ba.