Ana cin zarafin Yaran Makaranta a China

Yaran China Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Yaran China

Rashin matakai na tsaron lafiya a makarantun kwana na kasar China ya sa dalibai 'yan makaranta cikin wani hali na fuskantar cin zarafi da lalata da su.

Wannan dai sakamako ne na wani bincike da kungiyar ba da agaji ta Save the Children ta gudanar. Yara miliyan 30 ne dai ke halartar makarantun kwana a kasar ta China.

Ana yawan bayar da rahotanni a kafofin watsa labarai na kasar ta China na irin cin zarafin da Malamai ke yi ma Yaran, sai dai kuma babban abin damuwa shine irin yadda gwamnati ta ki mayar da kai ga wannan batu.

Karin bayani