A bai wa Buhari lokaci na gyara — Magoya baya

Magoya bayan Buhari Hakkin mallakar hoto
Image caption Magoya bayan Buhari

A Najeriya, yayin da ake ci gaba da murnar nasarar zaben Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, wasu magoya bayan sa sun ce akwai bukatar 'yan kasar su kasance masu hakuri saboda za a dauki lokaci kafin a samu biyan bukata a kasar.

Wasu fitattun magoya bayan Janar din a jihar Nasarawa sun ce al'amura da dama sun tabarbare a Najeriya kuma gyaransu zai dauki lokaci.

A gefe daya kuma, 'yan kasar ta Nijeriya na ci gaba da bayyana tarin burin da suke fatan sabon zababben shugaban kasar Muhammadu Buhari zai cika musu idan ya kama mulki.

Wata kungiyar Fulani ce da ake kira Jam Naati Fulbe ta ce bukatar ta ita ce shugaban kasar mai jiran gado ya duba matsalolin da makiyaya Fulani na kudu maso yammacin Najeriya ke fuskanta.

Karin bayani