Paladinawa sun ki karbar kudi daga Yahudawa

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Abbas ya ce Isra'ila ta zaftare musu kudi.

Shugaban Palasdinawa, Mahmoud Abbas, ya ki karbar daruruwan miliyoyin dala na haraji da Isra'ila ta sakar wa hukumar Palasdinawa.

Mr Abbas ya ce ya mayar da kudin ne saboda Isra'ila ta yanke wani kaso na kudin da ta ce bashin da kamfanoninta ke bin Palasdinawa ne.

Shugaban ya ce yawan kudin ya kai kashi daya bisa uku na kudaden da Palasdinu ke bin Isra'ilan.

Mr Abbas ya ce ko dai gwamnatin Isra'ila ta biya kudin gaba daya ko kuma ya kai kara gaban masu shiga tsakani, ko kuma kotun manyam laifuka ta duniya.

A watan Disamba ne Isra'ila ta fara yanke kudaden, bayan da hukumar Palasdinawan ta bayyana cewa za ta shiga cikin kasashen da ke kotun manyan laifuka ta duniya, ICC.