Kungiyar IS ta sako 'yan Yazidi 200

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption 'Yan Yazidi sun shiga tasku saboda 'yan kungiyar IS

Rahotanni daga arewacin kasar Iraki sun ce mayakan kungiyar IS sun sako mutane fiye da 200 'yan kabilar Yazidi da su ka sace.

Bayanai sun ce wadanda aka sako din tsofaffi ne da kuma marasa lafiya.

A cikin watan Janiaru ma mayakan sun sako wasu daga cikin mutanen da suke garkuwa da su.

An tilasta wa dubun-dubatar mabiya addinin Yazidi barin muhallansu a cikin watan Agusta, lokacin da mayakan I-S suka kaddamar da hare-hare a kauyukansu.

'Yan kungiyar IS na kallon mabiya addinin Yazidi a matsayin wadanda ke kan hanyar da ba ta dace ba.

Akwai wasu dubban mutane wadanda a yanzu haka suke hannun 'yan kungiyar IS daga cikinsu kuma akwai mata da kananan 'yan mata.