Jonathan ya yi gargadi game da haddasa rarrabuwa a Najeriya

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya

Yayinda Najeriya ke shirin zaben Gwamnoni da majalisun dokokin jihohi a ranar asabar mai zuwa, Shugaba Goodluck Jonathan ya bukaci 'yan kasar da su ci gaba da kasancewa masu zaman lafiya da hadin kai da kuma bin doka da oda.

A cikin wata sanarwa Shugaban yayi tir da wani kokarin da wasu yan siyasa da kungiyoyi da mutane ke yi na musgunawa wasu da kara ruruta zaman dar dar din siyasa domin haddasa rashin jintuwa a cikin al'uma sakamakon zaben Shugaban kasa da yan majalisar dokoki na kasa na ranar 28 ga watan Maris.

Shugaban ya bukaci dukanin wadanda suke haddasa rarrabuwar kai da bangaranci da kuma kiyayyar kabilanci a kasar bayan sakamakon zaben ranar 28 ga watan Maris da su daina, sannan su guji ababuwan da za su kai ga yin lahani ga kyakykyawar akidar demokuradiya da yan Najeriya ke fata.

Haka nan Shugaba Jonathan yayi tir da musgunawar da ake wa jami'an gwamnatin dake aiki a gwamnatinsa, sannan ya bukaci dukanin mutanen da lamarin ya shafa da su ci gaba da gudanar da aikinsu ba tare da nuna tsoro ba.

Shugaban ya ankaras da cewar kamata yayi wannan ya kasance lokaci na sasanta banbance banbancen siyasa domin amfanin hadin kan kasa da zaman lumana da ci gaba.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya ba za ta lamunci kokarin haddasa rikici a duk wani sashe na kasar don cimma wani burin siyasa ba.