An yi zanga-zanga kan harin Garissa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Kenya

A kalla mutane 2,500 ne suka gudanar da machi a Kenya domin nuna alhini bisa mummunan harin da mayakan Al-Shabbab suka kai a kan wata jami'a da ke garin Garissa.

An gudanar da macin ne a rana ta karshe ta zaman makokin mutane 147 din da suka mutu a harin wanda aka kai makon daya gabata.

Fiye da mutane dubu biyu ciki har da shugabannin addinai ne suka bi sahun macin da akayi a Garissa.

A Nairobi babban birnin kasar ta Kenya dalibai na daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zanga inda suke kira ga gwamnati da ta kara zage damtse wajen tabbatar da tsaro a kasar baki daya.

Wasu daga cikin su na cewa a basu bindiga domin su kare kansu idan har gwamnati ba zata iya ba.

Hassan Ole Naado na daga cikin majalisar koli ta malaman addinin musulunci a Kenya ya ce ana yiwa musulmai wani irin kallo a wasu sassa na kasar nan.

"Wasu 'yan kasar Kenyan wadanda ba asalin yan Somaliya ba zasu iya fuskantar kalubale kamar musulman da suke 'yan kalilan a wasu wurare." in ji Malamin.

Tuni dai aka gurfanar da wasu mutane biyar a gaban kotu wadanda ake zarginsu da hannu cikin harin.