Shin kada kuri’a na tasiri a Afrika?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zabe domin neman 'yanci

A cikin jerin wasikun da muke samu daga ‘yan jarida a Afrika, mai shirya fina-finai kuma mai yin sharhi a jaridu Farai Sevenzo, ya yi nazari a kan kimar kada kuri’a a bana.

Nigeria ta gabatar da zabenta na shugaba kasa. Dukkan masu sharhi na duniya dai na hasashen cewa ba za ta canza zani ba: Wanda ke kan mulki ne zai ci gaba.

Amma kayen da shugaba Jonathan ya sha a hannun Janar Buhari da kuma rungumar kaddara da ya yi, ya nuna cewa lallai shugaban ya cika alkawarinsa na ganin an yi zabe mai cike da adalci.

Wannan kyakkyawan misali ne abin kwatance a shekarar 2015, shekarar da kasashen Afrika da yawa za su gudanar da zabukansu.

Zambia ce kasar da ta fara gudanar da zabe a watan Janairu, sai kuma Lesotho wacce tayi na ta zaben gabannin lokacin da aka sanya. Hakan ya biyo bayan yunkurin juyin mulki da aka so a yi wa Firai Minista Thomas Thabane wanda ya yi barazanar ruguza zaman lafiyar kasar.

A wasu wuraren kuwa an ja hankalin mutane wajen raba musu riguna da buhunan shinkafa da alkawura kala-kala a kasashe kamar su Burkina Faso da Burundi da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Habasha da Guinea da Ivory Coast da Sudan da Tanzania da kuma Togo a lokacin yakin neman zabe na 2015.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu murnar nasarar zaben Janar Buhari a Nigeria

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir zai sha fama da ‘yan adawa kafin ya cimma burinsa na yin tazarce a wannan karon.

A hannu guda kuma, jaririyar kasa a Afrik,a Sudan ta Kudu ta dage zabenta na farko tun bayan samun ‘yancin kai, wanda ya kamata a yi shi a wannan shekarar, har sai shekara ta 2017 saboda tashe-tashen hankulan da kasar ke fama dashi.

A Jamhuriyar Afrika ta tsakiya kuwa, shekarar 2014 ta zamo ta zubar da jini, saboda yadda kasar ta rikice da rigingimun addini.

Zaben da za a yi a watan Yuli zai zamo wajen da mutane za su dinga mubaya’a ga siyasar addini amma akwai alamun lamarin zai jawo tashin hankali.