An kashe mutane 550 a Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu biyayya ga shugaba Hadi na jiran birne mutanen da suka rasu

Hukumar lafiya ta duniya ta ce kusan mutane 550 aka kashe a kazamin fadan da ake a Yemen a 'yan makonnin da suka gabata.

Hukumar ta ci gaba da cewa wasu mutanen kusan dubu daya da dari bakwai kuma sun samu raunuka a rikicin.

'Yan tawaye wadanda aka fi sani da Houthis da kawayensu na gwabzawa ne da dakarun da suke biyayya ga shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi wadanda ke samun goyon bayan dakarun kawancen da Saudiyya ke jagoranta .

Christophe Boulierac jami'i ne a asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya watau UNICEF ya ce rikicin da ake ya kara ta'azzara mummunan yanayin da kananan yara ke ciki a kasar.

Ya ce "Yara kananan na cikin wani mummunan yanayi a Yemen inda suke fama da rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin samun kula da lafiyar su. Kazalika rikicin na shafar karatun su. A saboda haka dole a samu mutuwar yara sosai saboda rashin magungunan da za a taimaka musu da su."

A bangare guda kuma, yayinda ake ci gaba da gwabzawa a Yemen, mutane na ci gaba da barin gidajen su.

UNICEF ta ce dubban mutane ne suka bar gidajen su a wasu yankunan kuma hanyoyin samar da ruwan sha sun lalace.