Boko Haram sun hallaka mutane a Chimbel

Wani dan garin wanda ya bukaci a sakaya sunansa yace yan Boko Haram din sun kai hari garin Chimbel da misalin karfe biyu na ranar Larabar nan inda suka kashe mutane suka kuma kona gidaje da dama.

Yace ko da a kwanakin baya ma 'yan Boko Haram din sun kai hari garin amma aka fatattake su. wannan karon sun sake yin gangami tare da motocin a kori kura da suka dorawa bindigogi.

A halin da ake ciki jama'a duk gudu babu kowa a garin kuma babu jami'an tsaro.

Wannan harin na zuwa ne a lokacin da sojojin Najeriya ke cewa suna samun galaba akan 'yan Boko Haram.