Burkina Faso ta hana jami'an Compaore takara

Hakkin mallakar hoto
Image caption Majalisar ta haramta wa duk wanda ya goyi bayan yi wa tsarin mulkin kasar gyara domin tazarcen Campaore rike mukami

Majalisar dokokin Burkina Faso ta haramta wa 'yan siyasar da ke da alaka da hambararren shugaban kasar Blaise Compaore tsayawa takarar shugabancin kasar a zabukan kasar da za a yi a shekarar nan.

Wata sabuwar dokar zabe da majalisar wucin gadin ta yi ta hana jami'an tsohuwar gwamnatin shugaban rike duk wani mukami, haka ma duk wani da ya goyi bayan kokarin yi wa kundin tsarin mulkin Burkina Fason gyaran fuska domin bai wa tsohon shugaban damar tsawaita mulkinsa, dokar ta shafe shi.

Kafin majalisar ta kada kuri'ar amincewa da dokar, 'yan sandan kasar sun kama wasu manyan 'yan siyasa na jam'iyyar Mr Compaore, da suka hada da wasu tsoffin ministoci uku.

A watan Oktoba na shekarar da ta wuce ne aka hambarar da Blaise Compaore daga mulki, bayan yunkurin da ya yi na gyara tsarin mulkin kasar domin yin tazarce ya haddasa tarzoma.