Mutane 80,000 za su iya mutuwa a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Annobar cututtuka masu bin jini za ta iya yaduwa tamkar wutar daji

Wani rahoto da gwamnatin Biritaniya ta fitar ya ce kimanin mutane 80,000 za su iya mutuwa idan har aka samu barkewar annobar cututtukan da suke bin jini da ba sa jin magani a Biritaniya.

Hukumar da ke kula da ayyukan gaggawa ta kasar ta ce ana tsammanin irin wannan annobar za ta iya shafar mutane 200,000, kuma akwai yiwuwar mutuwar mutane biyu cikin ko wadanne mutune biyar.

Rahoton ya kuma ce ana tsammanin za a samu yawaitar mace-mace daga wasu cututtukan daban wadanda ba sa jin magani.

Ya kuma yi gargadi cewa hadarin kamuwa da cutar zai iya sanya magungunan zamani su zama marasa tabbaci.

Rahoton ya kara da cewa ana tsammanin yaduwar cututtuka masu wuyar-sha'ani da ba sa jin magani za ta karu nan da shekaru 20 masu zuwa.

Rahoton ya ce, "Idan babu magungunan kashe kwayoyin cuta masu karfi, to ko da aiwatar da karamar tiyata zai iya zama mai hadari, wanda zai iya jawo doguwar jinya ko mace-mace na gaggawa."

A cewar rahoton yin dashen sassan jiki da tiyatar hanji da kuma bin wasu hanyoyin magance cutar daji zai daina yin tasiri wajen warkar da cuta.

'Zamanin duhun kai'

Rahoton -- wanda aka wallafa a watan Maris -- ya kara da cewa, "idan har annoba ta barke, to akwai yiwuwar mutane 200,000 za su kamu da cututtukan da suke bin jini wadanda ba za a iya magance su da magungunan da aka saba amfani da su ba; a sakamakon haka kimanin mutane 80,000 za su iya rasa rayukansu".

Ya ce gwamnatin Biritaniya tana jan ragamar aikin da hadin gwiwar abokan hulda na duniya domin shawo kan wannan matsala a duniya.

A baya dai, Firai Minista David Cameron ya yi gargadi cewa idan ba a dauki wani mataki na magance barazanar barkewar annobar cututtukan da ke bin jini ba, wadanda ba sa jin magani, akwai yiwuwar duniya za ta koma 'yar gidan jiya kamar lokacin da ba a samu ci gaba ba ta fuskar kiwon lafiya.

Babban jami'in lafiya na Ingila, Dame Sally Davies, ya kira wannan matsala da "annoba ce da za ta iya yaduwa kamar wutar daji."

Amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta a Biritaniya yana karuwa kuma a baya-bayan nan ne hukumar kula da lafiya ta kasar ta yi kira ga likitoci da su dinga sa ido kan yadda abokan aikinsu ke bai wa marasa lafiya magungunan ba tare da iyakance wa ba.