Tafida Mafindi ya koma APC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Isa Mafindi ya ce PDP ta yi mutuwar kwando, ba ta da sauran amfani

Mataimakin darektan yada labarai na yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, Alhaji Isa Tafida Mafindi, ya koma jam'iyyar APC.

Alhaji Tafida ya ce, ya yanke shawarar hakan ne domin PDP ta mutu kuma yana ganin ba za ta biya masa bukata ba a don haka ya bar ta zuwa APC.

Ba ya ga haka ya ce, zai yi aiki tukuru domin ganin APC ta ci kujerar gwamnan jiharsa ta Taraba.

Ya ce bayan da suka fadi zabe ya fahimci cewa da yawa wadanda suka yi aikin yakin neman zaben ba su yi tsakaninsu da Allah ba.

Tsohon kakakin na yakin neman zaben, ya ce zai je ya hadu da sauran 'yan PDP da suka koma APC domin su yi aikin ciyar da Najeriya gaba.