Iran ta bukaci a tsagaita wuta a Yemen

Hakkin mallakar hoto ISNA
Image caption Iranian President, Hassan Rouhani

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya bukaci a dakatar da luguden wuta a kan 'yan tawayen Houthi na Yemen da kasar Saudiyya ke jagoranta.

A cewarsa kuskure ne wannan yakin da ake yi.

Iran ta yi watsi da zargin da Saudiyya ke yi ma ta cewar ita ce ke horas da 'yan Houthi wadanda 'yan Shi'a ne.

A kan haka ne Iran ta bai wa karamin jakadan Saudiyya a Tehran sammaci domin ta gabatar da korafin ta.

A cikin Yemen, jiragen sama na yaki da Saudiyya ke jagoranta, sun kai hare-hare da dama a yankunan 'yan Houthi da ke arewaci da tsakiya da kuma kudancin kasar.