Tarihi: Kashe kwarkwatar ido a Lokoja

Image caption Mahadar Kogin Neja da na Benue a garin Lokoja

Garin Lokoja, fadar gwamnatin jihar Kogi da ke arewacin Najeriya na kunshe da muhimman kaya da kuma wuraren tarihi, musamman na zamanin Turuwan mulkin mallaka.

Image caption Karafan Iron of Liberty da ke nuna alamar kawo karshen cinikin bayi a Afrika

Wadannan wurare, idan aka alkinta su, a cewar masana za su samar da kudaden-shiga da kuma ayyukan yi masu yawa ga al'umar Najeriya. Sai dai masanan na kukan cewa saboda rashin sanin dadi da darajar yawon-bude-ido, 'yan kasar da dama ba sa ziyartar wadannan wurare na tarihi. Kamar yadda masana harkokin yawon bude-ido ke cewa, garin Lokoja shi ne rumbun wuraren tarihin Najeriya ta arewa, musamman zamanin mulkin mallaka, kasancewar har yanzu da ragowar shaida ko alamun wadansu muhimman abubuwan da suka wakana a wancan zamanin, kuma kasancewar garin hedikwatar Turawan Ingila ta farko a arewa, karkashin gwamna Lugga (Lord Luggard), kafin a kai ta Kaduna. Duk da cewa wasu daga cikin gine-gine da Turawa suka yi a garin sama da shekara 100 sun fara zama kufayi, har yanzu wasu daga ciki na ci gaba da wanzuwa, kuma ana amfani da su, yayin da aka kebe wasu zuwa kayan tarihi.

Image caption Gidan hutawar Gwamna Lugga, daga gefe ga mutum-mutuminsa da matarsa

Malam Nasidi wani masanin tarihin Nigeria ya ce “Wannan dutse na Mount Patti kamar yadda ka ke gani ga mutum-mutumin Luggard da matarsa Flora Shaw wacce ita ce ta bai wa kasar nan suna Nigeria, to nan dinnan gidan hutawarsa ne kuma kana iya hango baki daya garin Lokoja daga nan.” Mr Olowolayemo Joseph shi ne Babban Manajan da ke kula da Hukumar yawon bude-ido ta jihar Kogi, “A Lokoja aka fara yin abubuwa da dama ciki har da Firamare ta farko a arewa wacce aka kafata a shekara ta 1865, da asibiti na farko da kuma gidan yari.” “Kazalika a Lokoja ne kuma aka yi makabartar Turawa ta farko a arewa,” in ji Mr Joseph.

Image caption Kushewar sarkin Zazzau Aliyu Dansidi a Lokoja

Baya ga makabartar Turawa, akwai makwantan wasu sarakunan arewa da suka karasa rayuwarsu a garin, a wata unguwa da aka fi sani da Kabawa, wadda muka ziyarce ta da Mallam Tanimu Nasidi: ‘’A wannan unguwa aka ajiye yawancin sarakunan da su ka yi wa Turawa bara’a kuma da su ka mutu sai aka binnesu a nan.” Kusan kowace kushewa an kebe ta ne a gida ko fuloti na musamman, an kuma tanadi mutanen da ke kula da ita.

Wasu wuraren tarihin sun hada da wurin da aka yi biki hadewar da larduna suka yi wajen dunkulewar Najeriya, wato inda aka yi kasa-kasa da tutar Birtaniya aka daga ta Najeriya, da Majami'ar Anglican ta farko kuma mafi girma a arewa, wadda a harabarta aka kafa alamar haramta bauta ko cinikin bayi, inda aka kafa abin da aka fi sani da Iron of Liberty a Turance. Duk da muhimmancin wannan gari saboda abubuwan tarihin da ya kunsa, kukan da kwararru a harkar yawon-bude ke yi shi ne 'yan Najeriya da dama ko ba su san da wanzuwar kayan tarihin ba, ko kuma ba su san darajarsu ba. Kamar yadda Mr Olowolayemo Joseph ke cewa:

‘’Hatta 'yan bokonmu ba sa daraja abin da muke da shi. Sun gwammace su fita wajen Najeriya su kashe kudadensu maimakon su yi yawon bude-ido a gida. Ballantana galibin talakawan kasarmu, wadanda neman kudi ya rufe musu ido.

Image caption Makarantar Firamare ta farko a arewacin Nigeria tun 1865

Wasu ko hutun shekara-shekara ba sa yi, sun gwammace a biya su kudin hutun. Don haka jama'ar gari da dama da ke zaune baki-da-hanci da wadannan wuraren tarihi ba su ma taba ziyartarsu ba.”

Harkar yawon-bude-ido dai babbar harka ce, kasancewar tana kunshe da ribar-kafa, wato takan samar da kudaden shiga ga gwamnati, kana tana samar da ayyukan yi ga jama'a, saboda duk inda aka tara baki, to kasuwar masu otel-otel da ta 'yan tuwo da sufuri da 'yan canjin kudi da sauran dangoginsu kan bude.

Kuma wannan harka ita ce babbar kafar samun kudin-shigar wasu manyan kasashen duniya.

Najeriya dai ta fi dogara ne ga mai wajen samun kudin shigarta, Kuma ganin yadda farashin mai ya fadi a duniya, kwararru na sa ran cewa mahukuntan kasar za su mai da hankali wajen bunkasa sauran kafofin samun kudin-shiga, kuma watakila likafar yawon-bude ido ta yi gaba.