Zabe: An rufe kan iyakokin Nigeria

Image caption Nigeria ta hada kan iyaka da kashe hudu

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan, ya bayar da umurnin a rufe kan iyakokin kasar saboda zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da za a yi a ranar Asabar.

Sanarwa wacce ta fito daga ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce, dokar za ta soma aiki ne tun daga karfe 12 na daren ranar Laraba har zuwa 12 na daren ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce an dauki matakinne saboda a tabbatar da an yi zabe cikin lumana a fadin kasar.

A lokacin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a karshen watan Maris, an rufe kan iyakokin kasar domin kauce wa tashin hankali.

Nigeria ta hada kan iyaka da jamhuriyar Benin a bangaren yamma, sannan ta hadu da kasashen Kamaru da Chadi da Nijer a bangaren arewacin kasar.