Zabe: 'Yan sanda sun takaita zirga-zirga

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Babban sufeto janar na 'yan sandan Nigeria, Sulaiman Abba

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ba da umurnin takaita zirga-zirgar ababen hawa a jihohi 36 na kasar a ranar Asabar mai zuwa.

Sanarwar da Kakakin rundunar, Emmanuel Ojukwu ya fitar, ta ce dokar za ta soma aiki ne tun daga karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma.

Rundunar ta ce dokar ba ta shafi masu ayyukan jin kai ba da kuma motocin da hukumar zabe INEC ke amfani da su da kuma na jami'an tsaro.

Sanarwar ta ce ba za a takaita zirga-zirgar ababen hawa a birnin Abuja ba saboda babu zabe a birnin.

Rundunar ta ba da tabbacin cewa za ta yi iyaka kokarinta domin ganin an yi zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin na jihohi.

Sanarwar ta kuma bukaci mutane su ba da rahoton duk wasu abubuwan da suke ganin akwai tababa a kansu.