Amurka ta gargadi Iran kan batun Yemen

Mayakan Houthi a Yemen Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Houthi a Yemen

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya gargadi Iran a kan goyon bayan da take bai wa 'yan tawaye Houti dake yaki a Yemen.

A wata hira da aka yi da shi ta talabijin, Mr Kerry ya ce, Amurka za ta taimakawa duk wata kasa a Gabas ta tsakiya dake fuskantar barazana daga Iran.

A ranar Laraba, Iran ta tura, wasu jiragen ruwa na yaki biyu zuwa tashar jiragen ruwa ta Aden domin taimaka wa 'yan tawayen, wadanda ke fafata yaki domin kama iko da birnin.

Karin bayani