Boko Haram ta kai hari a kan Burutai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta kashe dubban mutane a Najeriya.

Rahotanni daga jihar Borno a Nijeriya na cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a garin Buratai da ke kan iyakar jihar Borno da Yobe.

Harin wanda aka kai ranar Juma'a da asuba ya haddasa asarar rayuka da kuma jikkata jama'a.

Barrister Jibrin Gunda shi ne mai ba da shawara ta fuskar shari'a ga kungiyar Civilian JTF a jihar Borno, kuma ya shaida wa BBC cewa kusan mutane bakwai suka mutu, yayin da mutane biyar suka jikkata.

A cewarsa, an tafi da wasu daga cikin mutanen da suka jikkata asibitin kashi da ke Kano domin yi musu magani.