Mutane dubu 25 na tuhumar Facebook

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Max Schrems, mai fafutukar kare bayanai

A cikin 'yan makonni masu zuwa ne wata kotu a Austria za ta yanke hukunci a kan ko tana da hurumin sauraron karar da wasu suka shigar a game da shafin sada zumunta na Facebook.

Wasu masu amfani da shafin Facebook su dubu 25, wadanda wani masanin shari'a Max Schrems ke jagoranta ne suka kai karar shafin Facebook saboda zarginsa da karya dokokin sirrin jama'a wajen yada bayansu.

An shigar da karar ce inda ake tuhumar shedkwatar shafin Facebook dake Dublin, wacce take tafiyar da shafukan mutane ba a Amurka da Canada ba.

Sai dai lauyoyin dake kare shafin Facebook sun bukaci kotun ta yi watsi da karar gaba daya, inda suka gabatar da hujjoji daga wata shari'a a kotu a Vienna ranar Alhamis.

Mista Schrems, mai fafutukar kare bayanai, ya ce sun shigar da karar ce saboda a kawo karshen yadda shafukan sada zumunci ke yi wa mutane leken asiri.

Mutanen sun shigar da karar ce saboda yadda shafin Facebook ya ke wa mutane leken asirin su idan suka latsa "like".

Sun kuma zargi shafin Facebook da hada baki da Prism, wani tsarin leken asiri da hukumar leken asiri ta Amurka ta kaddamar a 2007.

Masu shigar da karar wadanda suka hada da 'yan Burtaniya fiye da 900 suna bukatar diyyar dala 539 ko wanne mutun guda.