Sojoji sun kwato garuruwa hudu a Borno

Dakarun Nigeria sun kwato garuruwa da dama

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

Dakarun Nigeria sun kwato garuruwa da dama

Rundunar sojin Nigeria ta yi ikirarin kwato garuruwa hudu daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar, ta ce sojojin kasa, tare da hadin gwiwar sojojin sama sun sake kwato garuruwan Bita da Izge da Yamteke da kuma Uba wadanda ke kananan hukumomin Askira Uba da kuma Damboa.

A cewar kakakin, a lokacin gumurzun an kashe soja daya sannan wasu 10 sun samu raunuka a yayin da aka kashe 'yan Boko Haram da dama.

Rundunar ta ce ta kuma kwato makamai masu yawa daga hannun 'yan kungiyar sannan suna ci gaba da nausawa domin kwato dajin Sambisa inda ake zaton akwai sansanonin 'yan Boko Haram da dama.

Kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin sojin Nigeria din na kwato garuruwan.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 15,000 a Nigeria.