Jihohin da aka ja zare tsakanin APC da PDP

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jonathan ya kaye a hannun Janar Buhari

A karshen wannan makon, 'yan Nigeria za su zabi gwamnoni 29, makonni biyu bayan da Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya doke Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP.

Takarar za ta fi zafi tsakanin wadanda ke yi wa PDP takara da kuma 'yan APC.

Ga wasu daga cikin jihohin biyar da takarar ta fi zafi:

Lagos:

Ita ce cibiyar kasuwancin kasar, ta kasance karkashin mulkin 'yan adawa tun daga komawar kasar bin tafarkin demokuradiyya a shekarar 1999.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babatunde Raji Fashola na jihar Lagos

Jihar ta samu gwamnoni biyu musulmi a cikin shekaru 16 ciki har da Babatunde Fashola mai barin gado wanda ake ganin ya aiwatar da ayyukan ci gaban kasa.

A kokarin kawo daidaito, a yanzu Kiristoci biyu ne ke takarar kujerar gwamna a manyan jam'iyyun kasar watau Akinwumi Ambode na APC da kuma Jimi Agbaje na PDP.

Jam'iyyar PDP ta taka rawar gani a zaben shugaban kasa a Lagos, don haka zaben na ranar Asabar zai yi zafi sosai.

APC ta shiga cikin damuwa abin da ya tilasta wa zababben shugaban kasa, Muhammadu Buhari kai ziyara Lagos domin yin kamfe a wannan makon.

Dan takarar PDP na da farinjini tsakanin al'ummar Igbo wadda ke harkokin kasuwanci sosai a Lagos.

Idan har jam'iyyar APC ta sha kashi a Lagos, wadda ta fi kowacce yawan al'umma a kasar da kuma kudaden haraji masu dinbim yawa.

Rivers:

Ana kallon wannan fafatawar a matsayin kokarin samun iko a kan rijiyoyin mai na kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Amaechi mai barin gado

Jam'iyyar PDP na da karfi sosai a jihar, kuma an samu tashin hankali a lokacin yakin neman zabe, inda jam'iyyar APC ta ce an kashe mata mambobi 55.

Gwamna Rotimi Amaechi mai barin gado wanda aka zaba a inuwar jam'iyyar PDP shekaru hudu da suka wuce, a yanzu shi dan jam'iyyar APC ne kuma shi ne ya jagoranci yakin neman zaben Janar Buhari.

Wasu na kallonsa a matsayin mara kishin 'dan uwansa', Goodluck Jonathan

Amaechi ya zabi Dakuku Peterside a APC domin ya gaje shi amma kuma uwargidan shugaban kasa, Patience Jonathan ta na goyon bayan Nyesom Wike na jam'iyyar PDP.

Kalubalen da ke gaban duk wanda ya lashe zaben shi ne ya sasanta tsakanin manyan kamfanonin mai da kuma al'ummomin yankin wadanda ke korafin ana lalata musu muhalli.

Kaduna:

Wannan jihar ita ce cibiyar siyasar arewacin Nigeria kuma galibin tsofaffin 'yan Boko na da gida a jihar. Sai dai ta rabu gida biyu inda Musulmi ke bangaren arewa sai Kiristoci ke bangaren kudu.

Image caption Margayi Patrick Yakowa

An sha fuskantar rikici mai nasaba da addini ko kabilanci inda dubban mutane suka rasu tun daga shekarar 1999.

Jam'iyyar APC ta tsayar da Nasir El-Rufai, tsohon ministan Abuja wanda aka yabe shi saboda aikin zamanantar da birnin tare da rusa gine-ginen da suka saba ka'ida.

Gwamna mai ci, Mukhtar Ramalan Yero, wanda ya dare kan kujerar bayan mutuwar Patrick Yakowa na fuskantar matsin lamba saboda jam'iyyar APC ce ta lashe zaben shugaban kasa a jihar.

Duk wanda ya samu nasara zai fuskanci kalubalen tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'ummomin jihar musamman tsakanin Fulani makiyaya da kabilun kudancin jihar.

Taraba:

Za a kafa tarhi a jihar Taraba da ke makwabtaka da jamhuriyar Kamaru idan har Hajiya Aisha Alhassan ta jam'iyyar APC ta lashe zabe saboda za ta zama mace ta farko da ta hau kujerar gwamna a Nigeria.

Image caption Gwamna Danbaba Suntai ya na jinya tsawon sama da shekaru biyu

Tsohuwar ma'aikaciyar kotun, wacce Musulma ce za ta fuskanci kalubale daga Kiristocin jihar wadanda suka shafe shekaru 16 suna mulkin jihar.

Abokin hammayyarta, Darius Ishaku na jam'iyyar PDP wanda tsohon minista ne, ya na goyon bayan Kiristocin jihar kuma ana zargin Janar T Y Danjuma ne ke daukar dawainiyarsa.

Taraba ta kasance a rabe tsakanin Musulmi da Kirista kuma jihar na fuskantar matsaloli masu nasaba da kabilanci da kuma addinni.

Hajiya Aisha Alhassan na da karbuwa sosai tsakanin musulman jihar, amma kuma za ta iya fuskantar kalubale daga wadanda ke ganin bai dace mata su yi shugabanci ba.

Imo:

Jihar Imo wacce ke kudu maso gabashin kasar inda al'ummar Igbo suka fi rinjaye, ta bai wa jam'iyyar PDP kuri'u masu yawa a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya.

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Okorocha ne kadai gwamna APC a kudu maso gabashin kasar

Amma duk da haka ba za a ce gwamna Rochas Okorocha na jam'iyyar APC ba zai taka rawar gani ba. Koda yake jam'iyyarsa ta APC ba ta da karfi a yankin, amma dai yana da farin jini tsakanin al'ummar jihar.

Zai fafata da Emeka Ihedioha na Jam'iyyar PDP wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalisar wakilai sannan kuma yana da goyon bayan shugaban kasar mai barin gado, Goodluck Jonathan.