Pakistan ta zama 'yar-ba-ruwanmu a rikicin Yemen

Pakistan ta ce za ta ci gaba da taka rawar diflomasiyya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Pakistan ta ce za ta ci gaba da taka rawar diflomasiyya.

Majalisar Dokokin Pakistan ta amince da wani kuduri da zai sa kasar ta zama 'yar-ba-ruwanmu a rikicin da ake yi a Yemen duk da kiran da Saudiyya ta yi mata na ta shiga gamayyar kasashen da ke yi wa 'yan tawayen Houthi luguden wuta.

Majalisar ta bayyana cewa Pakistan "tana so" ta zama 'yar-ba-ruwanmu domin taka rawa ta hanyar diflomasiyya har a kawo karshen rikicin.

Sai dai 'yan majalisar sun kara da cewa kasarsu za ta bai wa Saudiyya goyon baya idan aka yi kutse a cikinta.

Ita dai kasar ta Pakistan -- wadda akasarin 'ya kasarta mabiya Sunna ne -- tana da dangantaka ta kut-da-kut da Saudi Arabia.

An kai wa kasar kayan agaji

Amma tana da mabiya Shi'a da dama, sannan tana da doguwar iyaka da Iran, wacce ministan harkokin wajenta ya je Islamabad ranar Alhamis domin tattaunawa kan rikicin.

A karon farko tun bayan barkewar rikicin, wani jirgin kungiyar bayar da agaji ta Red Cross dauke da kayan agaji ya sauka a birnin Sanaa.

Kungiyar ta ce kayayyakin sun hada da magunguna, da bandeji da kayan yin tiyata.