2015: 'Yan Nigeria da yawa ba sa fita zabe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu kada kuri'a a Najeriya

A yayin 'yan Nigeria ke shirin zaban gwamnoni da 'yan majalisar dokokin jihohi ranar Asabar din nan, wasu masana sun nuna damuwa game da yadda ake samun 'yan kasar da yawa da ba sa fita zabe.

A zaben shekara ta 2011 mutane da dama ne suka kaurace wa rumfunan zabe, kuma a wannan karon ma aka samu wasu mutane da dama da ba su fita zaben shugaban kasar da aka gudanar a makwanni biyun da suka gabata ba.

Dr Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa a jam'i'ar Abuja, ya ce akwai yiwuwar adadin masu zabe ya kara raguwa a zaben gwamnoni da ke tafe saboda jama'a sun fi dora fifiko a kan zaben shugaban kasa.

Ya dora alhakin wannan lamari a kan gazawar jam'iyyun siyasa na fadakar da jama'a muhimmancin zabe a kowanne mataki, inda ya ce "a ganina, zaben kananan hukumomi, yana da muhimmanci ga talakawa fiye da na shugaban kasa".