Yemen: MDD ta bukaci a hau teburin tattaunawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga dukkan bangarorin da suke da hannu a rikicin kasar Yemen da su mutunta dokar kasa da kasa.

Babban Sakataren Majalisar Ban Ki-moon ya ce dole ne bangarorin dake da hannu a rikicin su koma teburin tattaunawa a siyasance domin shawo kan lamarin.

Mai magana da yawun kwamitin kasa da kasa na kungiyar agaji da Red Cross, Sitara Jabeen ta ce lamarin na kasar Yemen yana gab da zama wani bala'i.

Jiragen yaki na dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta suna ci gaba lugudan wuta a wuraren da 'yan tawayen Houthi suke a yemen, a wani yunkuri na hana su ci gaba da dannawa, da kuma mai da shugaba Abdurabbuh Mansour na kasar da 'yan tawayen suka tilastama tserewa kan mulkinsa.

Sai dai shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya zargi kasar Saudi Arabiya da kisan kare dangi a matakin soji da ta dauka a kan 'yan tawayen Houthi a Yemen din.

Saudi Arabiya dai ta dade tana zargin Iran da taimakawa 'yan tawayen Houthi da makamai.