Zabe: Mutane hudu sun mutu a Kebbi

Image caption Mutane a Kebbi sun yi a kasa a tsare a raka

'Yan sanda a jihar Kebbi sun ce an hallaka akalla mutane hudu a cikin wani tashin hankali mai nasaba da zabe a kauyen Bayan Dutse da ke karamar hukumar Suru a jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Kebbi ce ta tabbatar wa da BBC hakan.

Sai dai bayanai sun nuna cewa a sauran sassan jihar an yi zabukan lami lafiya, kuma tuni aka fara rufe rumfunan zabe bayan kammala kidayar kuri'u.

Janar Sarkin Yaki Bello na PDP ne ke fafatawa da Sanata Atiku Bagudu na jam'iyyar APC.

A zaben shugaban kasa makonni biyu da suka wuce, Janar Buhar na APC ne ya lashe zabe a jihar Kebbi a yayin da gwamnan jihar, Saidu Usman Dakingari ya fadi takarar kujerar Sanata.