Obama zai gana da Castro na Cuba

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Barack Obama da Raul Castro

Shagaba Amurka Barack Obama da na Cuba Raul Castro za su zama shugabannin kasashen biyu na farko a cikin shekara 60 da za su gana ido da ido idan su ka hadu a Panama.

Ganarwar da za su yi na a wani bangare ne, na taron kasashen nahiyar Amurka, kuma zai kasance taro mafi girma tsakanin Washington da Havana tun lokacin da aka yi juyin-juya halin Cuba.

Daya daga cikin abubuwan za su tattauna a kai hadda batun sauye-sauyen siyasa a Cuba da Shugaba Obama yake bukata a yi.

Shugaba Castro ya na neman a janye takunkumin kasuwanci da aka saka a tsakanin kasashen biyu kuma a cire Cuba daga jerin kasashen da Amurka ta saka a matsayin masu daukar nauyin 'yan ta'ada.

Shugabanin biyu, sun yi musabiha kuma sun dan tattauna a lokacin da su ka gana na dan takaitaccen lokaci a ranar Juma'ar da ta gabata.

Tun da farko, shugaba Obama ya ce an kawo karshen lokacin da Amurka za ta dunga tsoma baki a kan irin abubuwan keta da ke wakana a kasashen Latin Amurka.