El-Rufai, Dankwambo da Ibikunle sun lashe zabe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Amosun na jihar Ogun shi ne na farko da aka sanar da sakamakon zaben sa a hukumance

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, INEC, ta sanar da Mr Ibikunle Amosun na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ogun.

Amosun, wanda shi ne gwamna mai ci a yanzu, ya doke dan takarar jam'iyyar PDP, Gboyega Isiaka.

Can kuma a Gombe, INEC ta sanar da Alhaji Ibrahim Hassan Dankwanbo a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Dankwambo na jam'iyyar PDP ya doke Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC.

A jihar Kaduna kuwa, Gwamna Mukhtar Ramalan Yero na jam'iyyar PDP ne ya amsa shan kaye a zaben na gwamna, inda ya kira abokin hammayarsa, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i, ya taya shi murnar nasarar da ya yi.

Hukumar zabe a jihar Kaduna ba ta riga ta bayyana El-Rufa'i a hukumance a matsayin wanda ya lashe zabe a jihar ba.