Kai Tsaye: Sakamakon zaben gwamnoni

Latsa nan domin sabunta shafin

Hakkin mallakar hoto Abdulrazaq Yusuf

Barkanmu da warhaka da kuma ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan sakamakon zaben Gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohin Najeriya.

  • Za ku iya aiko mana da yadda al'amura suke wakana a yankunanku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

16:52 Kakakin hukumar zaben Najeriya, INEC Mr Nick Dazang ya tabbatarwa BBC cewa ana kone-kone na tayoyi a kusa da babban ofishin INEC da ke Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom. Amma a cewarsa masu murna ne ke kone-kone, ba wai abin tashin hankali bane.

16:37 Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Katsina, ta sanar da Alhaji Aminu Bello Masari na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, inda ya doke Musa Nashuni na jam'iyyar PDP.

16:30 Sakamakon kuri'un da aka kada a zaben gwamna a jihar Sokoto, kuma aka bayyana a ofishin hukumar INEC ya nuna cewar shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar APC shi ne ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben.

16:20 Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Adamawa, Malam Nuhu Ribadu ya amsa shan kaye a zaben gwamnan jihar. Sakamakon da aka fitar a hukumance kawo yanzu ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar APC Sanata Bindowa Jibrilla ne ke kan gaba a yawan kuri'u.

Image caption Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya na cikin wannan cibiyar tattara sakamakon zaben gwamna a Kano

15:51 Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da Alhaji Ibrahim Hassan Dan kwambo na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Gombe. Ya doke Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC.

15:30 Hukumar zabe ta Najeriya- INEC ta ce an samu matsalar tashin hankali a wurare fiye da 60 wajen zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki da aka yi a kasar a ranar Lahadi.

15:25 Bayanai daga jihar Benue na cewa an sanar da sakamakon zabe na kananan hukumomi 15 daga cikin 24 da ke fadin jihar. Kuma jam'iyyar APC ce ke kan gaba a yawan kuri'u.

Image caption Gwamna Ramalan ya taya El Rufai murnar nasara a zaben gwamna

15:20 A hukumance, INEC ba ta bayyana wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kaduna ba. Amma an kamalla sanar da sakamako a zaben a kananan 15 daga cikin 23. Inda jam'iyyar APC ke da rinjayen kuri'u.

15:14 Gwamnan jihar Kaduna, Mukthar Ramalan Yero ya amsa shan kaye a zaben gwamna, inda ya kira abokin hamayyarsa, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na jam'iyyar APC domin taya shi murnar lashe zaben gwamnan jihar Kaduna.

15:10 Wakilinmu a Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta lashe kujerun 'yan majalisar dokoki na jihar guda 35, kamar yadda hukumar zaben kasar ta ba da sanarwa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Amosun ya samu goyon bayan Janar Buhari da Sanata Bola Ahmed

14:50 Sakamakon zaben ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar PDP Gboyega Isiaka ne ya zama na biyu inda ya samu kuri'u 201,440 sai kuma Sanata Akin Odunsi na jam'iyyar SDP da ya samu kuri'u 25,826. INEC ta ce Gwamna Amosun ya lashe zabe a kananan hukumomi 11 daga cikin 20 da ke jihar.

14:40 Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Ogun ta sanar da gwamna Ibikunle Amosun na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar. Babban jami'in tattara sakamakon zaben a jihar, Farfesa Duro Oni ya ce Amosun ya lashe zaben da kuri'u 306,988.

13:50 Wakilinmu Abba Muhammad Katsina ya bayyana cewa hukumar zabe a jihar ta sanar da sakamakon zabe a kananan hukumomi 32 daga cikin 34 na jihar. Kuma jam'iyyar APC ce ta samu kuri'u mafi rinjaye. A yanzu ana jiran sakamakon zaben gwamna na karamar hukumar Faskari, sai kuma karamar hukumar Dan Musa da aka dage zaben.

Sakonni daga BBC Hausa WhatsApp:

  • "A nan karamar hukumar Dan musa da ke jahar katsina, an dage zaben wasu rumfuna da ke cikin garin amma a sauran wurare ba a samu wata matsala ba sosai," in ji Umar Timoti katsina.
  • "Abin da ya faru a zaben jihar Ribas, ba zabe aka yi ba rubutawa aka yi. Sannan kuma 'yan tayar da kayar bayan sun ci zarafin mutane a Fatakwal," sako daga Ahmad Isa Jalingo.
  • "Ina kira ga 'yan takara da su yi koyi da Shugaba Goodluck Jonathan idan sun sha kaye, su taya wadanda su ka yi nasara murna," in ji Salisu Lawal kaya jihar Zamfara.

12:40 Wakilinmu a Kaduna, Nurah Muhammad Ringim ya ce an sanar da sakamakon zaben gwamna a kananan hukumomi 15 daga cikin 23 na jihar. Kuma jam'iyyar APC ce ke kan gaba. A yanzu an tafi hutu a ofishin INEC na Kaduna, sai karfe 3 na rana za a ci gaba da sanar da sakamakon.

12:24 Allon sakamakon zaben gwamna a jihar Kano ya nuna cewa, jam'iyyar APC na da kuri'u 546,754 a yayinda jam'iyyar PDP ke da kuri'a 138,429. An fitar da sakamakon zabe na kananan hukumomi 19 daga cikin 44.

Image caption Allon sakamakon zabe a Kano

12:10 Wakilinmu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce an sanar da sakamakon a kananan hukumomi da dama, inda Dr Abdullahi Ganduje ke da kuri'u mafi rinjaye a kan na dan takarar PDP, Salihu Sagir Takai.

11:55 Wakilinmu a Lagos, Umar Shehu Elleman, ya ce hukumar zabe a jihar Oyo a hukumance ta bayyana sakamakon zabe a kananan hukumomi 21 na jihar. Dan takarar jam'iyyar APC kuma gwamna mai ci, Abiola Ajimobi ne keda kuri'u mafi rinjaye.

Image caption Masu zabe a jihar Jigawa. Muhammad Annur Muhammad ne ya dauko mana hoton a Dutse.

Sakonni daga BBC Hausa Facebook:

"Kusan kowa ka gani ya zaku yana jiran sakamakon abin da ya zaba da fatan Allah ya futo mana da alkhairi," sako daga Sagir Dutse Hakika.

"Mu kam a Jigawa Alhamdulillah, an yi zabe lafiya sai dan abind a ba a rasa ba. Mun zura ido muna jiran sakamakon abin da muka zaba," in ji Babangida Chairman Kakabori Hadejia.

"A gaskiya mu a nan jihar Kano zabuka sun gudana lafiya sakamako ka wai muke jira," in ji Ibrahim Mansur Ungogo

"Muna taya 'yan uwanmu 'yan Najeriya murnar yin zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jahohi cikin lumana, kuma Allah ya sa shugabanni da aka zaba su yi aiki tsakaninsu da Allah," in ji Boyes Mubi Saudiya.

11:25 Hukumar zabe a jihar Sokoto ta sanar da sakamakon zabe a kananan hukumomi 14 daga cikin 23 da ke fadin jihar. Sakamakon a hukumance na nuna cewa, shugaban majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar APC na kan gaba a yawan kuri'u idan aka kwatanta da kuri'un da abokin hammayarsa na PDP, Alhaji Abdullah Wali ya samu.

Image caption Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza a ofishin tattara sakamakon zabe a Birnin Kebbi

11:00 Bayanai daga sansanin 'yan gudun hijirar Bama da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno na cewa an soma kada kuri'a a sansanin Yalwa. Hassan Lamini ya ce komai na tafiya lami lafiya inda jama'a ke kan layuka suna kada kuri'arsu.

10:50 Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya bayyana cewar Izuwa karfe 11 saura kwata ba a soma sanar da sakamakon zaben gwamna a hukumance ba a jihar Kebbi. Sai dai bisa dukkan alamu ana gab da soma bayyana sakamakon a ofishin INEC da ke Birnin Kebbi, saboda turawan zabe sun riga sun hallara.

10:00 Sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomi takwas a Kaduna na nuna cewa dan takarar jam'iyyar APC, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na kan gaba a yawan kuri'un da hukumar INEC ta bayyana.

09:55 Sakamakon zaben gwamna a jihar Kaduna da aka bayyana sun hada da na kananan hukumomin Soba, Kudan, Makarfi, Birnin Gwari, Lere, Kajuru, Kubau, Kauru, Kagarko da kuma Sabon Gari.

Image caption Har yau Lahadi an ci gaba da kada kuri'a a jihar Ribas

09:50 Wakilinmu a Kaduna, Nurah Muhammed Ringim a ofishin tattara sakamakon zabe na INEC a jihar Kaduna ya ce kawo yanzu an bayyana sakamakon zabe a kananan hukumomi takwas daga cikin 23 na jihar.

09:35 Shugabar INEC a jihar Ribas, Gesila Khan ta bayyana cewa an soke zabe a wasu wurare a jihar saboda satar akwatinan zabe da kuma magudin zabe. Bayanai sun ce an samu tashin hankali a wurare da dama a jihar lokacin zaben na jiya.

09:30 Hukumar zabe a jihar Ribas da ke yankin Naija Delta mai arzikin man fetur ta ce a yau Lahadi an ci gaba da kada kuri'a a wasu mazabu tara wadanda ba a iya gudanar da zabe ba a jiya Asabar.