APC ta lashe zaben jihar Plateau

Image caption Jam'iyyar APC ta kayar da PDP wacce ke mulkin jihar Plateau tun daga shekarar 1999.

Hukumar zaben jihar Plateau ta ayyana dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC, Mr Simon Lalong a matsayin mutumin da ya lashe zaben gwamnan jihar.

Mr Lalong ya lashe zaben ne da kuri'u fiye da 564,89, yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Senator Gyang Pwajok, ya samu kuri'u 520,572.

Wannan shi ne karo na farko da jam'iyyar adawa ta kayar da jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ta Plateau tun da Najeriya ta dawo kan turbar dimokradiyya a shekarar 1999.

Wasu masu sharhi na ganin cewa kayen da jam'iyyar ta PDP ta sha a jihar yana da nasaba da rashin iya mulkin gwamnan jihar, Jonah Jang, wanda ake zargi da kin biyan albashin ma'aikata da rashin samar da abubuwan more rayuwa.

Sai dai gwamnan ya sha cewa yana kyautata rayuwar mazauna jihar.