Ana samun karuwar bakin haure a Italiya

Hakkin mallakar hoto Italiancoastguard press office
Image caption Ana ceto bakin haure a tekun Italiya.

Masu tsaron gabar tekun Italiya sun ce an samu karuwar bakin hauren da ke kokarin tsallakawa cikin kasar daga kogin Baharrum.

Jiragen ruwan kasar sun ceto mutane fiye da 4,000 a kwanaki uku da suka wuce.

A ranar Lahadi kadai an ceto lalatattun jiragen ruwa guda 22 dauke da mutane.

Wani kwale-kwale -- da yake dauke da mutane 150 -- ya nitse wani waje mai nisan kilomita 120 tsakanin sa da gabar tekun Libya, inda aka samu gawarwakin bakin haure guda tara, kuma an kuma ceto mutane a kalla 140.

Ana zaton za a samu karin bakin haure da za su yi kokarin tsallaka tekun idan yanayi ya inganta.