An tafka kura-kurai a zaben Nigeria - EU

Image caption An tafka kura-kurai a zaben gwamnoni a Nigeria in ji EU

Tawagar masu sa ido a kan zabukan Najeriya ta kungiyar tarayyar Turai - EU ta ce an tafka kura kurai a zabukan gwamnoni da 'yan majalisar jihohin da aka yi a krashen makon jiya.

Tagawar ta bayyana haka ne a cikin rahoton wucin gadi da ta fitar ranar Litinin.

Tawagar sa idon ta kuma bayar da shawarwari a kan gyare-gyaren da suka kamata a yi kafin da kuma lokacin zabuka na gaba.

Sai dai masu sa idon sun yaba da yadda aka gudanar da zabukan a wasu jihohin kasar inda ba a samu matsaloli masu yawa ba.