Samsung zai fuskanci karancin sabuwar wayarsa ta S6

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Apple na gasa da Samsung

Samsung ya fara sayarda wayarsa samfurin S6 amma kamfanin yana ta fafutukar ganin cewa wayoyin sun isa a kasuwa

Kodayake Samsung ya yi hasashen riba a sabuwar wayar amma ya damu game da lokacin da ake dauka na kera wayar.

Kwararru sun ce hakan zai iya sa masu sayen wayoyin dole sai sun yi oda sannan su jira.

Samsung na fuskantar gasa mai karfi daga Apple yayinda kuma wayoyi masu arha da ake samarwa a China suma ke yi kasancewa wani kalubale ga Samsung

Wani mai yin sharhi akan wayoyin salula Thomas Husson ya fadawa BBC cewa kamfanin zai fuskanci matsala idan har wahalar dake tattare da samar da sabuwar wayar shi ne yake janyo karancin wayar