"'Yan matan Chibok suna nan a raye"

Hakkin mallakar hoto SALKIDA PHOTO
Image caption Salkida ne dan jarida daya tilo da ya je wajen da ake tsare da 'yan matan Chibok.

Wani dan jarida -- wanda aka san yana da dangantaka ta kut-da-kut da shugabannin Boko Haram -- ya ce 'yan matan Chibok fiye da 200 da kungiyar ta sace suna nan a raye, kuma cikin koshin lafiya.

A wata hira ta musamman da Ahmad Salkida ya yi da BBC, ya ce 'yan matan na da matukar muhimmanci a wajen kungiyar ta Boko Haram saboda, a cewarsa, sun amince da akidojin kungiyar.

Ahmed Salkida ne dan jarida daya tilo da ya ziyarci dajin da 'yan Boko Haram suke tsare da 'yan matan bayan an sace su, lokacin da ya yi yunkurin shiga tsakanin 'yan Boko Haram da gwamnatin Najeriya domin ganin an kubutar da su.

Ya yi ikirarin cewa an yi watsi da batun shiga tsakanin da ya so ya yi bisa umarnin da gwamnatin Tarayyar Najeriyar ta bayar na dakatar da hakan.

Sai dai gwamnatin ta sha cewa a shirye take ta bi duk wata sahihiyar hanya ta sulhuntawa da kungyar ta Boko Haram.