Ana tunawa da 'yan matan Chibok

Image caption Yau shekara guda kenan, tunda aka sace 'yan matan makarantar Chibok.

An yi wata zanga- zanga a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya domin tunawa da 'yan matan makarantar Chibok, wadanda a ranar Talata suka cika shekara guda a hannun Boko Haram.

Masu yin jerin gwanon sun ce za su yi kwanan zaune da nuna alamu ta hanyar motsi da jiki a Najeriya, da kuma wasu kasashen waje.

Shugaban kasar mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, ya ce wasu 'yan matan ba za a same su ba, amma zai yi iyakar kokarinsa domin ya dawo da su wurin iyayensu.

A ranar Litinin ne wata mata da ke garin Gwoza da ke arewa maso gabashi Najeriya ta ce ta ga wasu daga cikin 'yan matan makonni uku da suka wuce.

An yi amannar cewa 'yan Boko Haram sun sace a kalla mata sama da 2000 tun daga karshen shekarar 2014 zuwa yau.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service