Ta'addanci: Cuba ta yaba wa Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Obama da Raul Castro na Cuba

Gwamnatin Cuba ta yi marhabin da matakin da Shugaba Obama ya dauka na cire ta daga jerin kasashen da ta dauka masu daukar nauyin ta'addanci, bayan sama da shekaru 30.

Ma'aikatar harkokin kasashen waje a Havana, babban birnin kasar ta Cuba, ta bayyana matakin da cewa abu ne mai kyau, amma kuma ta ce, daman tun da farko ma bai kamata a ce kasar tana cikin jerin sunayen ba.

Wannan shi ne mataki na baya bayan nan na Shugaba Obama na dawo da hulda tsakanin kasashen biyu.

Sai dai kuma dan majalisar dattawa na Florida, kuma mai fatan samun tikitin yi wa jam'iyyar Republic takarar shugabancin Amurkan, Marco Rubio, ya yi Allah-wadai da matakin.

Ya ce, ''Cuba kasa ce mai daukar nauyin ta'addanci. Sun bayar da mafaka ga wadanda suka tsere wa shari'ar Amurka, ciki har da wanda ya kashe dan sanda a New Jersey sama da shekaru 30 da suka wuce.''