Zawarawa sun fi kamuwa da ciwon zuciya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani bincike da aka gudanar a Amurka ya nuna cewa wadanda aurensu ya mutu sun fi kamuwa da ciwon zuciya fiye da takwarorinsu masu aure.

Binciken ya nuna cewa lamarin mutuwar aure ya fi yi wa mata illa, kuma illar na raguwa idan har suka sake yin aure.

Binciken - - wanda aka wallafa a wata mujalla mai suna Circulation, ya nuna cewa matsananciyar damuwar da ake samu a dalilin mutuwar aure na yin illa ga lafiyar jiki.

Wata gidauniya da ke bayar da tallafi ga masu ciwon zuciya ta Biritaniya ta yi kira da a sake zurfafa bincike tun kafin a sanya mutuwar aure cikin manyan dalilan kamuwa da ciwon zuciya.

Tuni dama aka gano cewa mutuwar wani masoyi na kusa, wato dan uwa ko ‘yar uwa zai iya jawo mummunan ciwon zuciya.

Yanzu haka wata tawaga a jami’ar Duke ta nuna makamancin wannan sakamako bayan mutuwar aure.

A lokacin da ake gudanar da binciken a tsakanin shekarar 1992 da 2010, mutum daya daga cikin uku, na kashe aurensu a kalla sau daya.

Akwai yiwuwar kashi 24 cikin 100 na matan da aurensu ya taba mutuwa sau daya su kamu da ciwon zuciya fiye da matan da suka yi ta sake aure bayan mutuwar na farkon. Adadin da ke nuna kashi 77 cikin 100.

A bangaren maza kuwa, idan mutum ya saki matarsa sau daya yana fuskantar kashi 10 cikin 100 na hatsarin kamuwa da ciwon zuciya, idan kuwa saki uku ya yi mata, to yana fuskantar kashi 30 cikin 100 na kamuwa da ciwon zuciya.

Daya daga cikin masu binciken, Farfesa Linda George, ta ce “Hatsarin ya fi yawa idan har mutum yana da hawan jini ko ciwon siga, don haka ta nan yake farawa; lamarin mai girma ne.”

Amma me ya sa ake fuskantar wannan matsala?

Masu binciken sun gano cewa sauye-sauyen da ake samu a yanayin rayuwa kamar su raguwar samun kudin batarwa ba za su iya bayyana girman hatsarin ba.

Farfesa George ta shaida wa BBC cewa “Hasashena shi ne matsananciyar damuwa tana yin illa ga sassan jiki”.

A yayin da magani ke iya rage hatsarin kamuwa da hawan jini, to babu hanyar magance radadin mutuwar aure cikin sauki.

Sai dai masu binciken sun bayar da shawarar cewa aminai na kut da kut su dinga kasance wa tare da mutum domin rage radadin.

Farfesa Jemy Pearson na gidauniyar da ke bayar da tallafi ga masu ciwon zuciya ta Biritaniya yace, “Mun dade da sanin cewa damuwarmu na iya shafar lafiyar zuciyarmu. Wannan binciken ya nuna cewa mutuwar aure na iya zama silar ciwon zuciya.”

"Amma sakamakon bai yi bayani sosai ba don haka ana bukatar karin hujjoji kafin a yanke hukuncin cewa mutuwar aure zai iya jawo ciwon zuciya.”