Sabon rikici ya barke a Ukraine

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Fada ya sake kacamewa a gabashin Ukraine

Sabon rikici ya barke a gabashin Ukraine, kwana guda bayan da aka sake hobbasar amfani da diplomasiyya wajen karfafa yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tangal-tangal.

Wani mai magana da yawun sojin kasar yace an kashe musu jami'an su guda shida sannan an shafe daren jiya ana musayar wuta.

Rahotanni sun ce ana cigaba da gwabzawa a kauyen Shyrokyne wanda ke wajen garin Donetsk.

A tattaunawar da suka yi a daren jiya a Berlin, ministocin harkokin wajen kasashen Jamus da Faransa da Rasha da kuma Ukraine sun nuna damuwar su a kan ruruwar wutar rikicin.

Sannan kuma sun amince da a janye manyan makamai daga gabashin Ukraine.

Ministan harkokin waje na jamus, Frank Walter Stenmeier ya shaidawa manema labarai cewa, daga ciki makaman da za a janye, har da tankokin yaki.

“Abinda aka shawarta shi ne dagane da matsanancin yanayin da ake ciki a Ukraine, a yau mun amince da cewa ba janye makamai kawai ba, duk wasu muggan makamai dole a janye su.”