Dole a ceci 'yan gudun hijira - MDD

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan ci-ranin Afrika na sayar da rayukansu a kokarin tsallaka wa Turai

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hada karfi da karfe domin ceto rayukan dimbin 'yan ci-ranin da ke kokarin zuwa Turai daga Afrika, bayan da wani jirgin ruwa ya kife dauke da kimanin mutane 400.

Kakakin jami'in kula da 'yan gudun hijira na Majalisar, Laurens Jolles, ya shaida wa BBC cewa an gaza a kokarin da ake yi a baya-bayan domin ceto 'yan ci-ranin.

Hukumar hijira ta duniya ta ce tuni mutane 500 suka rasa rayukansu a bana a kokarinsu na shiga Turai, yawan da ya ninka na bara sau goma a dai-dai irin wannan lokacin.

A ranar Laraba ne kuma wasu 'yan gudun hijirar da yawa suka isa tsibirin Sicily da ke Italiya.