Ana alhinin hadarin jirgin ruwan Korea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yawancin wadanda suka mutu a hadarin dalibai ne

'Yan kasar Korea ta kudu suna tunawa da sama da mutane dari uku da suka mutu sakamakon hadarin jirgin ruwa na Sewol.

Shugabar kasar, Park Geung-Hye ta sanar da cewa za a tsamo jirgin daga karkashin teku.

Da take magana kan bukatar da dangin wasu da hadarin ya rutsa da su, shugabar ta ce, za a dago jirgin a rana mafi kusa da za a iya.

Shugaba Park tana magana ne a lokacin da ta kai ziyara tsibirin Jindo domin mika ta'aziyyarta ga iyalan wadanda suka mutu a hadarin, amma iyalan sun ki ganawa da ita.

Haka kuma iyalai da dangin wadanda suka mutum da ke cikin fushi sun hana Frai ministan Korea ta Kudun Lee Wan Koo, isa wurin da ake jimamin tunawa da daliban a garinsu.