A kara kaimi don kawar da Ebola - Obama

Hakkin mallakar hoto
Image caption A na kokarin kawar da Ebola

Shugabanin kasashen Laberiya da Saliyo da kuma Guinea--kasashe uku wadanda cutar Ebola ta fi kamari, sun gana da shugaba Obama a fadar gwamnatin Amurka inda suka tattauna akan ci gabar da aka samu a kan kokarin da ake yi na kawar da bazuwar cutar.

Obama ya ce duk da dai cewar yawan yaduwar cutar ya ragu, dole ne kasashen duniya su cigaba da taimakawa kasashen uku har a kawar da cutar.

Shugaban na Amurka da sauran shuwagabanin kasashen Afrika uku sun kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi na kare bullar ta a nan gaba.

Sama da mutane dubu goma ne suka rasa rayukan su tun bayan bullar cutar a watan Disambar a 2013.

Shugabanin kasashen Afrikan guda uku suna Washington domin su halarci ganawar da za a yi da asusun lamuni na majalisar dinkin duniya da bankin duniya.