Cuba ba 'yar ta'adda ba ce-Obama

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Shugaban kasar Amurka, Obama da Catro na Cuba

A wata wasika da shugaba Obama ya aike wa majalisar dokokin kasar ta Amurka ya ce a tsawon watanni shida ba bu wata shaida da ta nuna cewa kasar Cuba tana da alaka da ta'addanci.

A zamanin mulkin Fidel Castro, a 1982, kasar ta Amurka ta ayyana sunan Cuba a rukunin kasashe masu taimaka wa ta'addanci da suka hada da Syria da Iran da kuma Sudan.

Hakan yasanya Amurkar ta kakaba wa kasar takunkumin hana yin kasuwanci da Cuba.

A dai makon da ya gabata ne shugaba Obama ya sadu da shugaban kasar Cuba, Raul Castro a taron kolin kasashen yankin karebiya a Panama.