Al-Shabaab na daukar matasan Kenya aiki

Image caption Kungiyar Al-Shabaan

BBC ta gano cewa kungiyar Al-Shabaa ta Somaliya tana daukar matasa a kasar Kenya domin zama mambobinta.

A wani gari da ake kira Isiolo, an samu rahoton batan sama da matasa ashirin, wadanda daga bisani suka kirawo iyayensu, suka shaida musu cewa sun shiga kungiyar ta Al Shabab.

Wakilin BBC na gabashin Afrika ya ce wadannan rahotanni suna kara tsoratar da masu aikin lekan asiri a kan cewar akwai wata sabuwar hanyar da kungiyar ta kirkira domin shigar da matasa cikinta.

Makwanni biyu da suka gabata, mutane kusan 150 suka rasu a wani hari da mayakan kungiyar suka kai kan jami'ar garin Garissa, kuma an gano daya daga cikin maharan dan kasar ta Kenya ne.