Bikin Kabilar Mbum da ke Kamaru

Kabilar Mbum mazauna Adamawan Kamaru sun karbi bakuncin 'yan uwansu mazauna kasashen waje a wurin bikin al'adarsu da kuma nuna wasannin gargajiya da ake kira "Mgbor Yanga".

Wannan shi ne karo na 913 da aka gudanar da bikin tun shekara ta 933, lokacin da aka fara kafa masarautar wannan kabila a Adamawan Kamaru bayan kakanninsu sun taso daga kasar Yamen a kan dawakai.

Wannan bikin kuma na bai wa Mbumawa damar ganawa da junansu, su kuma tattauna batutuwan da suka kamata wurin ci gabansu da kuma karfafa dankon zumunci.

Tun shekara ta 1997, wannan bikin na gudana ne karkashin jagorancin Belaka Salihu Saw Mbum, wanda shi ne Sarki a yanzu.

A ganawar da ya yi da 'yan kabilar tasa yayin bikin na wannan karo, sarki Salihu ya ce, "Cikinmu nan kowa yana da matsaloli, kuma tunda ba a kasa daya muke zama ba, ba zamu san matsalolin juna ba sai a irin wannan haduwa, sai mu tattauna yadda za mu magance matsalar da kuma yadda za mu samu ci gaba."

Mbumawa dai na zaune ne a yankuna daban-daban na nahiyar Afrika a kasashe irinsu Kamaru da Chadi da Tripoli ta kasar Libya, sai dai a cewar sarkin nasu ba su cika hada kai sosai ba.

"Matsalarmu ita ce rashin hadin kai, amma yanzu muna kokarin hada kai sosai saboda mun fahimci muhimmancin hakan," in ji Sarki Salihu.

Babban abin sha'awa ga wannan kabila ta Mbum ita ce yadda jama'arsu ke zame musu wakilai a duk in da su ka sami kansu musamman ta fuskar ayyukan zamani.

Abubakar Umaru wani Malamin makaranta ne da shi ma ya ke bayar da gudunmowarsa wajen ganin ci gaban wannan kabila ta Mbum.

"Na kan je wajen sarki duk shekara na shaida masa irin ci gaban da muke samu ta fuskar karatu da matsalolin da muke cin karo da su kuma na ba shi shawara a kan abin da ya kamata a yi."

A lokacin da ake gudanar da wannan biki, ana raye-raye da wake-wake na gargajiya, ana kuma baje-kolin kayan tarihi da na al'adu tare da wasannin gargajiya.

Merama na Yariman Ghanha, wata dattijiya ce da ta gwanance wajen kitse kan mata, kuma ita ce mai yi wa matar sarki kitso, kuma sana'ar kitso na daga cikin fasahar da ake bajewa a yayin bikin al'adar.

"Wannan sana'ar kitso gadon zuriyarmu ce don haka tun ina yarinya na iya sosai."

Daga cikin kayayyakin gargajiya da aka nuna a wajen bikin akwai wukake da gatari da kwalli da fata.

Shi ma Sa'idu Sarkin gargajiya wanda yana daya daga cikin wadanda suka baje kayan ya shaida wa BBC cewa, "Mu kan shiga daji ne mu nemi irin wadannan kayayyaki, kuma mafi yawan yaranmu yanzu ba su san kayan ba shi ya sa muke kawo su wajen wannan biki domin su gani su san tarihi".

A wajen wannan biki dai mutanen kabilar Mbum suna hawa wani tsauni mai dimbin tarihi da ke garin Ngoundare cibiyar Adamawan Kamaru da ake kira "Tsaunin Rau", wanda a cewarsu shi ne ainihin wajen zaman kakanninsu a wancan lokacin.

Sarki Salihu ya ce "Muna zuwa wannan tsauni ne domin 'yan baya su san tarihinmu wanda hakan ma zai kara mana dankon zumunci."