'Yan Ghana sun gurfana a kotu kan safarar hodar ibilis

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutanen sun yi yunkurin shigar da hodar ibilis cikin Ghana ne daga Bolivia.

Wasu 'yan Ghana biyu sun bayyana a gaban kotu a Accra, babban birnin kasar a kan tuhumar da ake yi musu ta kokarin shigar da kusan tan shida na hodar cocaine cikin kasar daga Bolivia.

Mutanen biyu, daya dan kasuwa, daya kuma jami'in hukumar hana fasa-kauri, dukkaninsu sun ki amince wa da zargin na yunkurin shiga da hodar ta iblis ta tashar jirgin ruwa ta Tema.

A watan jiya ne aka kama cocaine din a Bolivia, an boye ta a daruruwan buhunan takin zamani.

Yankin Yammacin Afrika dai ya kasance wata muhimmiyar hanyar safarar muyagun kwayoyi da ake satar fitowa da su daga Latin Amurka zuwa kasashen yammacin Turai.