Jirgin ruwa ya sake nitsewa da 'yan cirani 40

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Immigrants being rescued by Coastguards.

Kafofin watsa labaran Italiya sun ce a kalla 'yan cirani 40 ne suka nitse a kogin Bahar Rum a kokarinsu na tsallake tekun su shiga Turai.

Rahotannin sun shaida wa 'yan sandan Italiya cewa lalataccen jirgin da ke dauke da 'yan ciranin ya nitse ne a Bahar Rum.

Masu tsaron tekun Italiya sun bayyana cewa an ceto bakin haure kusan 900 a ranar Alhamis.

Tarayyar Turai, EU ta ce zai yi wuya a hana bakin haure kokarin zuwa Turan.

A farkon makon nan an samu bakin haure 400 daga Afrika ta arewa da suka nitse a tekun Bahar Rum.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Tarayyar Turai da sanya rayukan 'yan ci ranin cikin hadari saboda dakatar da ceto su daga fadawa tekun da ta yi.