Amurka na kirkiro jiragen yaki samfurin farin dango

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagoran aikin Lee Mastroianni, ya ce ba a taba kai wa irin wannan mataki na kirkirar jirgi maras matuki ba

Sojin ruwa na Amurka suna aikin kirkirar jirgin sama na yaki maras matuki wanda tarinsa zai kasance cikin wani sunduki da za su rika fita kamar farin dango a lokacin yaki.

Jiragen za su rinka tashi da kansu ne kuma su nufi kan abokan gaba.

Da zarar fika-fikan jiragen sun bude za su nufi wurin abokin gaba kamar fari, suna kai hari.

A shekarar 2016 ne dai ake sa ran kammala aikin kirkirar jiragen.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Amurka na shan suka daga masu kare hakkin dan adam kan yadda take amfani da jiragen yaki marassa matuka, duk da yadda suke kai hari ba tare da kuskure ba a yawancin lokaci.

Masu rajin na cewa duk da haka a wasu lokutan jiragen na kashe mutanen da ba su ji ba basu gani ba.

Hukumar kula da aikin kira jiragen ta ce saboda basu da girma sosai, za a iya daukansu a jiragen ruwa ko jirgin sama ko motoci.

Duk da cewa za a iya sa kwamfuta ta tsara kuma ta kai harin jiragen, to amma za a sa wani mutum da zai rika sanya ido a kai.

Jagoran aikin Lee Mastroianni, ya ce ba a taba kai wa irin wannan mataki na kirkirar jirgi maras matuki ba.